1.4 KiB
1.4 KiB
ƙarfin hali, yin ƙarfin hali
Ma'ana
Wannan kalma "ƙarfin hali" ma'anarta yin wani abu gabagaɗi mai wuya, mai bantsoro, da kuma hatsari.
- Wannan kalma "ƙarfin hali" yana bayyana mutum wanda yake nuna ƙarfin hali, wanda yake yin abin dake dai dai ko yana jin tsoro ko an matsa masa ya bari.
- Mutum yakan nuna ƙarfin hali sa'ad da ya fuskanci tashin hankali ko ciwon jiki tare da ƙarfi da naciya.
- Wannan furci "kayi ƙarfin hali" ma'anar shi ne "kada kaji tsoro" ko " ina tabbatar maka cewa komai zai zama lafiya."
- Lokacin da Yoshuwa yake shirin shiga cikin ƙasan nan mai hatsari ta Kan'ana, Musa ya karfafa shi ya "dage yayi ƙarfin hali."
- Wannan kalma "ƙarfin hali" za a iya fasara ta haka, ko "mai ƙarfin hali" ko "marar tsoro" ko "mai gabagaɗi."
Bisa ga yadda za a yi amfani da shi a rubutu, idan an ce "kayi ƙarfin hali" za a iya fassara shi haka, "kayi ƙarfi cikin hankalinka" ko "ka ƙarfafa" ko "ka tsaya daram." A yi magana da ƙarfin hali" za a iya fassara shi haka, "yi magana gabagaɗi" ko "yi magana ba tare da tsoro ba ko "yi magana da ƙarfi."
(Hakanan duba: gabagaɗi, gargaɗi, tsoro, ƙarfi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Maimaitawar Shari'a 01:37-38
- 2 Sarakuna 18:19-21
- 1 Tarihi 17:25
- Matiyu 09:20-22
- 1 Korintiyawa 14:1-4
- 2 Korintiyawa 07:13
- Ayyukan Manzanni 05:12-13
- Ayyukan Manzanni 16:40
- Ibraniyawa 03:12-13
- Ibraniyawa 13:5-6