1.1 KiB
1.1 KiB
tabbata, tabbatarwa
Ma'ana
Waɗannan kalmomi "tabbata" ko "tabbatarwa" ana nufin faɗi ko "haƙƙaƙe wani abu gaskiya ne" ko amincewa" ko "dogara."
- A cikin Tsohon Alƙawari, Allah ya gaya wa mutanensa zai "tabbatar" da alƙawarisa da su. Ma'ana, yana cewa zai cika alƙawaran da yayi cikin yarjejeniyar.
- Idan aka "tabbatar" da sarki ana cewa zaɓen da aka yi ya zama sarki an yarda da shi kuma mutane sun goyi baya.
- Idan za a tabbatar da abinda wani ya rubuta ma'anar shi ne abin da an rubuta gaskiya ne.
- Tabbatar da bishara, ma'anar shi ne koyawa mutane game da labari mai daɗi na Yesu ta hanya mai ban sha'awa da zai nuna gaskiya ne.
- Idan an yi rantsuwa mai kwari domin "tabbatarwa" ma'anar shi ne a furta abu gaba gaɗi ko "a rantse cewa wani abu gaskiya ne ko za a iya dogara gareshi.
- Waɗansu hanyoyin fasara "tabbatarwa" sune, "faɗin abu yadda yake gaskiya" ko "gwada amincinsa" ko "tabbatarwa" ko "alƙawari," ya danganta ga nassi.
(Hakanan duba: alƙawari, rantsuwa, dogara)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tarihi 16:15-18
- 2 Korintiyawa 01:21
- 2 Sarakuna 23:3
- Ibraniyawa 06:16-18