1.1 KiB
1.1 KiB
ta'aziya, mai ta'aziya
Ma'ana
Waɗannan kalmomi "ta'aziya" da "mai ta'aziya" ana nufin taimakon wani mutum ne wanda yake shan wahala a jiki ko a ruhu.
- Mutumin da yake ta'azantar da wani mutum ana kiran sa "mai ta'azantarwa."
- A cikin Littafin Tsohon Alƙawari, kalman nan "ta'aziya" ana amfani da shi a faɗi yadda Allah yake nuna alheri da ƙauna ga mutanensa yana kuma taimakon su lokacin wahalarsu.
- A cikin Sabon Alƙawari, an ce Allah zai ta'azantar da mutanensa tawurin Ruhu Mai Tsarki. Waɗanda suka karɓi ta'aziyar sukan iya sadar da wannan ta'aziya ga wasu kuma masu shan wuya.
- Wannan furci "mai ta'azantar da Isra'ila" ana nufin Almasihu ne wanda zai zo ya kuɓutar da mutanensa.
- Yesu ya ce da Ruhu Mai Tsarki "Mai Ta'aziya" wanda yake taimakon masu bada gaskiya ga Yesu.
Shawarwarin Fassara
- Ya danganta ga yadda yake a nassi, " za a iya fassara "ta'aziya" haka, "sanyaya ciwo" ko "taimako."
(Hakanan duba: ƙarfafa, Ruhu Mai Tsarki)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tassalonikawa 05:8-11
- 2 Korintiyawa 01:04
- 2 Sama'ila 10:1-3
- Ayyukan Manzanni 20:11-12