874 B
874 B
ɗan ƙasa
Ma'ana
Ɗan ƙasa mutum ne wanda yake zaune musamman cikin birni, ƙasa, ko mulki. Ana nufin mutum musamman wanda sananne ga hukuma cewa mazaunin wurin ne.
- Ya danganta bisa ga yadda yake cikin rubutu, za a iya fassarawa haka "mazaunin wuri" ko "mazauni sananne."
- Ɗan ƙasa zai iya zama a yankin da take cikin gundumar wata babbar mulki da sarki yake mulki akai. Ga misali, Bulus ɗan ƙasar mulkin Roma ne, wadda ta ƙunshi larduna da yawa kuma dabam dabam; Bulus ya zauna cikin ɗaya daga cikin waɗannan lardunan.
- Haka ma a misalce, masu gaskatawa da Yesu ana kiransu "'yan ƙasar" sama domin za su zauna a can watarana. Kamar ɗan ƙasar ƙasa, Kristoci 'yan mulkin Allah ne.
(Hakanan duba: masarauta, Bulus, lardi, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 21:39-40
- Ishaya 03:03
- Luka 15:15
- Luka 19:14