920 B
920 B
Tarihi
Ma'ana
Wannan kalma "tarihi" manufarta shi ne rubutattun labarbaru game da abubuwan da suka faru na dogon lokaci.
- Litattafai guda biyu na Tsohon Alƙawari ana kiransu "Littafin Tarihi na Farko" da Littafin Tarihi na Biyu."
- Littattafan da ake kira "Tarihi" an rubuta tarihin mutanen Isra'ila ne, ya fara da jerin sunayen mutane a kowanne tsara tun daga Adamu.
- "Littafin Farko na Tarihi" ya bada labarin ƙarshen rayuwar Sarki Saul da ayyukan sarautar Sarki Dauda.
- "Littafin Tarihi na Biyu" ya rubuta akan sarautar Sarki Suleman da wasu sarakuna da dama, akwai kuma ginin haikali da rabuwar mulkin Isra'ila ta arewa daga mulkin Yahuda ta kudu.
- Karshen Littafin Tarihi na Biyu ya bada labarin farawar kwashewa zuwa Babila.
(Hakanan duba: Babila, Dauda, hijira, masarautar Isra'ila, Yahuda, Suleman)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tarihi 27:24
- 2 Tarihi 33:19
- Esta 10:1-2