750 B
750 B
manyan firistoci
Ma'ana
Manyan firistoci wasu mahimman shugabannin addinin Yahudawa ne a lokacin da Yesu yayi rayuwa a duniya.
- Manyan firistoci sune aka rataya masu kula da dukkan abubuwan da ake buƙata domin sujada a haikali. Sune kuma suke da hakin lura da kuɗin da aka bayar domin haikali.
- Sune sama a muƙami da iko fiye da ƙananan firistoci. Babban firist ne kaɗai yake da iko fiye da su.
- Manyan firistoci suna cikin wasu maƙiyan Yesu kuma sun iza shugabannin Roma su kama shi su kashe.
Shawarwarin Fassara
- Wannan furci "manyan firistoci" za a iya fasara shi haka "firistoci dake bisa firistoci" ko "firistoci masu bishewa" ko "firistoci masu mulki."
- A tabbatar an fassara wannan kalma ta fita dabam da "babban firist."