1.1 KiB
1.1 KiB
ƙidaya
Ma'ana
Wannan kalma "ƙidaya" ana magana ne akan ƙayadadden ƙidaya domin sanin yawan mutane a cikin al'umma ko mulki.
- Tsohon Alƙawari ya rubuta lokatai da dama sa'ad da Allah ya umarta a ƙidaya mutanen Isra'ila, misali lokacin da Isra'ilawa suka fara barin Masar da kuma kafin su shiga Kan'ana.
- Yawancin lokaci dalilin ƙirga mutane shi ne don a san mutane nawa ne yakamata su biya haraji.
- Misali, a wani lokaci a cikin Fitowa aka ƙirga mazajen Isra'ila domin kowanne ɗayansu ya biya rabin shekel saboda lura da haikali.
- Lokacin da Yesu yake ɗan jariri, gwamnatin Roma tayi ƙidaya domin ƙirga dukkan mutane waɗanda suke mazaunnan yankin mulkinsu, domin a buƙace su su biya haraji.
Shawarwarin Fassara
- Wasu hanyoyin fassara wannan kalma zai haɗa da waɗannan "ƙidayar sunaye" ko "ɗaukar sunaye" ko "rubutawa."
- Wannan furci "yin ƙidaya" za a iya fassara shi zuwa "shigar da sunayen mutane" ko "ɗiban mutane" ko "rubuta sunayen mutane."
(Hakanan duba: ƙasa, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 05:37
- Fitowa 30:12
- Fitowa 38:26
- Luka 02:03
- Littafin Lissafi 04:1-4