760 B
760 B
raƙumi, raƙuma
Ma'ana
Raƙumi wani dabba ne, mai ƙafafu huɗu da tozo ɗaya ko biyu a bayansa.
- A zamanin Littafi Mai Tsarki, raƙumi shi ne dabba mafi girma da ake samu a Isra'ila da lardunan kewaye.
- Ana amfani da raƙumi musamman domin ɗaukar mutane da kaya.
- Wasu ƙungiyoyin mutane suma suna amfani da raƙumi domin abinci amma ba Isra'ilawa ba saboda Allah ya ce raƙuma marasa tsabta ne kuma ba za a ci su ba.
- Raƙuma masu daraja ne saboda zasu iya matsawa da sauri cikin yashi kuma zasu iya zama babu abinci da ruwa na tsawon makwonni da yawa a lokaci guda.
(Hakanan duba: nauyi, tsabta)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tarihi 05:21
- 2 Tarihi 09:1-2
- Fitowa 09:1-4
- Markus 10:25
- Matiyu 03:04
- Matiyu 19:23-24