897 B
897 B
cin hanci, toshi
Ma'ana
"Cin hanci" shi ne bada wani abu mai daraja, misalin kuɗi, domin ka rinjayi wannan mutumin ya yi wani abin rashin gaskiya.
- Sojojin da suka yi tsaron kabarin Yesu daba kowa a ciki an basu cin hanci kuɗi domin suyi karya game da abin da ya faru.
- Wani lokaci akan ba ma'aikatan hukuma cin hanci domin su ƙyale laifi ko su jefa kuri'a yadda ake so.
- Littafi Mai Tsarki ya hana bayarwa da karɓar cin hanci.
- Kalmar nan "cin hancii" za a iya fasara shi haka "biyan rashin gaskiya" ko" biya don ayi ƙarya" ko "lada domin karya dokoki."
- Za a iya fassara "bada cin hanci" da kalma ko furci mai ma'ana haka, "biya domin a rinjayi wani" ko "biya domin a yi alfarma marar gaskiya" ko " a biya don a sami alheri.
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sama'ila 08:1-3
- Littafin Mai Wa'azi 07:7
- Ishaya 01:23
- Mika 03:9-11
- Littafin Misalai 15:27-28