ha_tw/bible/other/breastplate.md

1.1 KiB
Raw Permalink Blame History

sulke, sulkaye, ƙyallen ƙirji

Ma'ana

Wannan kalma "sulke" na nufin wani kayan yaƙi ne da yake rufe gaban ƙirji ya tsare soja a lokacin yaƙi. Kalmar nan "ƙyallen ƙirji " yana nufin wani ƙyalle ne musamman da babban firist na Isra'ila yake sakawa akan fuskar ƙirjinsa.

  • "Sulke" da soja ke amfani da shi ana yinsa da itace, ƙarfe, ko fatar dabba. An yi shi domin a kare kibau, mãsu, ko takkuba daga sukar ƙirjin soja.
  • "Ƙyallen ƙirji" da babban firist na Isra'ila ke sawa anyi shi da ƙyalle yana kuma da wasu duwatsu masu daraja da aka manna a kansa. Firist yakan sa wannan sa'ad da yake hidimarsa ga Allah a haikali.
  • Wasu hanyoyi na fassara "sulke" za a haɗa da waɗannan "makari na ƙarfe mai rufe ƙirji" ko "makamin yaƙi mai kare ƙirji."
  • Wannan abin da ake ce da shi "ƙyallen kirji" za a iya fassara shi da kalmomin nan haka, "suturar firist mai rufe kirji" ko "rigar firist" ko "ƙyallen gaba na suturar firist."

(Hakanan duba: makami, babban firist, sokewa, firist, haikali, mayaƙi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tasalonikawa 05:08
  • Fitowa 39:14-16
  • Ishaya 59:17
  • Wahayin Yahaya 09:7-9