1.8 KiB
1.8 KiB
gurasa
Ma'ana
Gurasa abinci ne da ake yinsa daga gari cuɗe da ruwa da mai sai ayi ƙullu. Wannan ƙullun za a yanyanka a cuccura su sa'annan a gasa.
- Sa'ad da kalmar nan "curi" tana ita kaɗai, ana nufin "curin gurasa" ne.
- Akan yi ƙullun gurasa yawancin lokaci da wani abin da yake sa shi ya kumbura, kamar gamin yisti.
- Za a iya yin gurasa ba tare da gamin yisti ba saboda haka ba zai tashi ba. A cikin Littafi Mai Tsarki ana ce da wannan "gurasa marar gami" ana amfani da shi domin abincin idin ƙetarewa na Yahudawa.
- Da shike gurasa shi ne babban abinci na mutane da yawa a lokacin Littafi Mai Tsarki, wannan kalma ana amfani da ita cikin Littafi Mai Tsarki a kamanta dukkan abinci.
- Wannan kalma "gurasar da aka miƙa ga Allah" yana magana akan curin gurasan nan goma shabiyu da aka sa akan tebur na zinariya a rumfar taruwa ko haikali wadda hadaya ne ga Allah. Waɗannan gurasa kabilun Isra'ila ne goma shabiyu kuma don firist ne kaɗai zai ci. Za a iya fassara wannan haka "gurasar da ta nuna Allah yana zaune tsakiyar su."
- Wannan misalin kalmar, "gurasa daga sama" ana faɗin wannan farin abinci na musamman da ake kira "manna" wanda Allah ya tanada domin Isra'ilawa lokacin da suke ta yawo a hamada.
- Yesu kuma ya kira kansa "gurasar da ta zo daga sama" da kuma "gurasar rai."
- Lokacin da Yesu da almajiransa suke cin abincin Idin Ƙetarewa tare kafin mutuwarsa, ya kwatanta gurasa marar gami na Ƙetarewa da jikinsa da za a ƙuje a kuma kashe akan gicciye.
- Sau da yawa wannan kalma "gurasa" za a iya fassarata ace "abinci."
(Hakanan duba: Ƙetarewa, rumfar sujada, haikali, gurasa marar gami, yisti)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 02:46
- Ayyukan Manzanni 27:35
- Fitowa 16:15
- Luka 09:13
- Markus 06:38
- Matiyu 04:04
- Matiyu 11:18