785 B
785 B
Littafin Rai
Ma'ana
Wannan furci "Littafin Rai" ana ambatar inda Allah ya rubuta sunayen dukkan waɗanda ya fansa ya kuma basu rai madawwami.
- Wahayin Yahaya ya ambaci wannan littafi ya ce "Littafin Ɗan Rago na Rai." Za a iya fassara shi haka "littafin rai na Yesu, Ɗan Ragon Allah." Hadayar Yesu akan gicciye ya biya hakin zunuban mutane domin mu sami rai madawwami ta wurin bangaskiya a cikinsa.
- Wannan kalma "littafi" zai iya zama da ma'ana haka "naɗaɗɗen littafi" ko "wasiƙa" ko "rubutu" ko ƙaiyadaddar takarda," Zai iya yiwuwa hakanan ko a misalce.
(Hakanan duba: madawwami, ɗan rago, rai, hadaya, naɗaɗɗen littafi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Filibiyawa 04:03
- Zabura 069:28-29
- Wahayin Yahaya 03:5-6
- Wahayin Yahaya 20:11-12