1019 B
1019 B
sharewa, gogewa
Ma'ana
Waɗannan kalmomi "sharewa" da "gogewa" kalmomi ne waɗanda ma'anarsu shi ne cirewa gabaɗaya ko hallaka wani abu ko wani mutum.
- Waɗannan furci za a iya amfani da su ta hanya mai kyau, kamar idan Allah ya "goge" zunubai ta wurin gafartawa ya kuma zaɓa ya manta da su.
- Ana kuma yin amfani da su ta hanyoyi marasa kyau, kamar idan Allah ya "gogewa" ko "share" wasu mutane, ya hallaka su saboda zunubansu.
- Littafi Mai Tsarki ya yi magana akan "gogewa" ko "share" sunan mutum daga littafin rai na Allah, wato wannan mutum ba zai sami rai madawwami ba.
Shawarwarin Fassara:
- Ya danganta ga yadda yake cikin nassi, waɗannan maganganu za a iya fassara su a ce, "a jefar da" ko "a cire" ko "a hallaka gabaɗaya" ko "a cire gabaɗaya."
- Sa'da da ana magana akan cire sunan wani mutum daga littafin Rai, za a iya fassara wannan haka, "cirewa daga" ko "gogewa."
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Maimaitawar Shari'a 29:20
- Fitowa 32:30-32
- Farawa 07:23
- Zabura 051:01