1.1 KiB
1.1 KiB
shekara, shekaru
Ma'ana
Idan an yi amfani da kalmar nan "shekara" kamar yadda aka saba yi, a cikin Littafi Mai Tsarki ana nufin wani tsawon lokaci na kwanaki 354 ne. Bisa ga tsarin kalandar wata wanda ya danganta ga lokacin da wata ke ɗauka ya kewaye duniya.
- Shekara guda a cikin kalandar wata na zamani ya kai kwanaki 365 a raba su watanni 12, bisa ga tsawon lokaci da duniya ke ɗauka ta kewaye rana.
- A cikin dukkan tsarin biyu shekara na da watanni 12. Amma da ƙarin wata na 13 wani lokaci a shekara ta kalandar wata domin shekara takan gaza da kwana goma sha ɗaya dana shekara ta rana. Wannan yakan taimaka wajen sa kalandojin su jera tare.
- A cikin Littafi Mai Tsarki kalmar nan "shekara" ana amfani da ita a nuna lokacin da wani sha'ani na musamman ya faru. Misali, "shekara ta Yahweh" ko "a shekarar fari" ko "shekara ta alherin Ubangiji" A cikin abubuwa haka, "shekara" za a iya fasarata zuwa "lokaci" ko "lotonsa" ko "sa lokaci."
(Hakanan duba: wata)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 2 Sarakuna 23:31
- Ayyukan Manzanni 19:8-10
- Daniyel 08:01
- Fitowa 12:02