671 B
671 B
sati, mako, makonni
Ma'ana
Wannan kalma "sati ko mako" ana nufin tsawon lokaci da ya kai kwana bakwai.
- A tsarin ƙirga lokaci na Yahudawa, sati guda yakan fara da maraicen ranar Asabar ya ƙarasa da maraicen ranar Asabar mai zuwa.
- A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "sati ko mako" wani tsawon lokaci ne da ake amfani da shi domin a misalta wasu lokatai haɗaɗɗu bakwai, kamar shekaru bakwai.
- Bikin Makonni' idi ne na girbi dake ɗaukar sati bakwai bayan idin Ƙetarewa. Shima ana kiransa "Fentikos."
(Hakanan duba: Fentikos)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 20:7-8
- Maimaitawar Shari'a 16:09
- Lebitikus 23:15-16