826 B
826 B
rana, ranaku, kwanaki
Ma'ana
Wannan kalma "rana" ana nufin wani lokaci na tsawon awa 24 idan an fara daga faɗuwar rana. Ana kuma yin amfani da ita wajen kwatanci.
- Ga Isra'ilawa da Yahudawa "rana" takan soma da faɗuwar ranar, kuma ta ƙare a faɗuwar washegari.
- Wani lokaci "rana" ana amfani da ita domin a misalta tsawon lokaci mai nisa, kamar "ranar Yahweh" ko "kwanakin ƙarshe."
- Wasu yare za su yi amfani da wasu furci su fassara waɗannan misalan ko su fassara "rana" ba tare da bada misalai ba.
- Wasu fassarar kalmar nan "rana" za a haɗa har da "lokaci" ko "yanayi" ko "sha'ani" ko "wani abin dake faruwa" ya danganta ga nassi.
(Hakanan duba: ranar hukunci, ranar ƙarshe)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 20:06
- Daniyel 10:04
- Ezra 06:15
- Ezra 06:19
- Matiyu 09:15