931 B
931 B
kwando, kwanduna, kwando cike
Ma'ana
Wannan kalma "kwando" wani daron zuba kaya ne da aka saƙa shi da wani abu.
- A lokacin Littafi Mai Tsarki, watakila ana saƙa kwanduna da tsire-tsire masu ƙarfi, kamar su itatuwan da aka ɓare rassansu ko ƙirare.
- Za a iya dalaye kwando da katsi domin ya iya iyo.
- Sa'ad da Musa yake jariri, mahaifiyarsa ta saƙa kwando ta shafe shi da katsi ta saka jaririn a ciki yana fito tsakanin ciyayin iwa a Kogin Nilu.
- Wannan kalma da aka fassara "kwando" a wancan labari ita ce kalmar da aka fassara ta a matsayin "jirgi" ana nufin kwale-kwalen da Nuhu ya gina. Ma'anar fassararsu ɗaya ce a yadda aka yin amfani da su dukka biyun wato, "abin sa kaya a ciki dake iyo."
(Hakanan duba: akwati, Musa, Gokin Nilu, Nuhu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 2 Korintiyawa 11:33
- Ayyukan Manzanni 09:25
- Amos 08:01
- Yahaya 06:13-15
- Littafin Alƙalai 06:19-20
- Matiyu 14:20