743 B
743 B
bali
Ma'ana
Wannan kalma "bali" sunan wata tsaba ce da ake amfani da ita wajen yin waina.
- Shi tsiron bali yana da kara mai tsawo da kai a bisansa inda ƙwayoyin suke fita ko girma.
- Bali ya fi yi da kyau a yanayi mai ɗumi saboda haka ake girbinsa a farkon damina.
- Sa'ad da aka casa bali, za a raba tsabar da ake ci da ƙaiƙayinta marar amfani.
- Tsabar bali kanta za a niƙata ta zama gari, sa'annan a kwaɓa ta da ruwa ko mai a yi waina.
- idan ba a san bali ba, za a iya fasara shi haka "hatsin da ake kira bali" ko "hatsin bali."
(Hakanan duba: hatsi, sussuka, alkama)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tarihi 11:12-14
- Ayuba 31:40
- Littafin Alƙalai 07:14
- Littafin Lissafi 05:15
- Wahayin Yahaya 06:06