1.5 KiB
1.5 KiB
taro, tarurruka, tattarawa, taruwa
Ma'ana
"Taro" shi ne idan ƙungiyar mutane sun haɗu domin su tattauna akan matsaloli ko bada shawarwari da ɗaukar matakai.
- Taro zai iya zama shiryayyen ƙungiya da aka haɗa ta akan tsarin dake din-dindin, ko kuma zai iya zama ƙungiyar mutane da suka haɗe tare na gajeren lokaci domin wani dalili na musamman ko wani sha'ani.
- A cikin Tsohon Alƙawari akwai wani irin taro na musamman da ake kira "keɓaɓɓen taro, inda mutanen Isra'ila za su taru su yiwa Yahweh sujada.
- Wani lokaci wannan kalmar "taro" na nufin Isra'ilawa ɗungum a ƙungiyar su.
- Babbar taruwar sojoji maƙiya wani lokaci ana ce da shi "taro." Wannan za a iya fassara shi a ce "rundunar sojoji."
- A cikin Sabon Alƙawari, taron shugabannin Yahudawa 70 a manyan birane kamar Yerusalem sukan hallaru domin su zartar da shari'a da sasanta jayayya tsakanin mutane. Sanannen sunan taron nan shi ne "Sanhedirin" ko kuma "majalisa."
Shawarwarin Fassara:
- Ya danganta ga nassin, "taro" za a iya fassara shi ya zama "taruwar musamman" ko "taron jama'a" ko "majalisa" ko "sojoji" ko "babbar ƙungiya."
- Sa'ad da aka yi amfani da kalmar nan "taro" domin Isra'ilawa gabaɗaya, za a iya fassara shi zuwa "mutanen dake tare" ko "mutanen Isra'ila."
- Wannan faɗar, "dukkan taro" za a iya fassara shi haka "dukkan mutane" ko "dukkan ƙungiyar Isra'ilawa" ko "kowa da kowa."
(Hakanan duba: majalisa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sarakuna 08:14
- Ayyukan Manzanni 07:38
- Ezra 10:12-13
- Ibraniyawa 12:22-24
- Lebitikus 04:20-21
- Nehemiya 08:1-3