591 B
591 B
maharbi, maharba
Ma'ana
Wannan kalma "maharbi" na nufin ƙwararren mutum mai iya harbi da baka da kibiya kayan yaƙi.
- A Littafi Mai Tsarki, maharbi yawancin lokaci mai yaƙi ne wanda yake amfani da baka da kibiya ya yi faɗa cikin rundunar mayaƙa.
- Maharba muhimmiyar ƙungiya ce a cikin rundunar Asiriyawa.
- Wasu harsuna mai yiwuwa suna da wani suna domin wannan kamar haka, "mutumin baka."
(Hakanan duba: Asiriya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sama'ila 31:1-3
- 2 Tarihi 35:23-24
- Farawa 21:20
- Ishaya 21:16-17
- Ayuba 16:13
- Littafin Misalai 26:9-10