669 B
669 B
fushi, yin fushi, haushi
Ma'ana
"Yin fushi" ko a ce "ina da fushi" ana nufin rashin gamsuwa, cakuna da tashin hankali game da wani abu ko gãba da wani.
- Sa'ad da mutane suka yi fushi, yawancin lokaci zunubi ne da son kai, amma wani lokaci fushi ne mai adalci domin an yi shi ne gãba da rashin adalci da ya auku.
- Fushin Allah (ana kiransa "hasala") yana nuna zafin rashin jin daɗinsa game da zunubi.
- Wannan furci "cakuna don ayi fushi" yana nufin "tayar da ɓacin rai."
(Hakanan duba: hasala)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Afisawa 04:26
- Fitowa 32:11
- Ishaya 57:16-17
- Yahaya 06:52-53
- Markus 10:14
- Matiyu 26:08
- Zabura 018:08