1.0 KiB
1.0 KiB
jakada, jakadai, wakili, wakilai
Ma'ana
Jakada wani mutum ne da aka zaɓa ya wakilci ƙasarsa a wajen wasu baƙin al'ummai. Ana kuma iya fasara wannan kalma a ce "wakili."
- Jakada ko wakili yana miƙa saƙonni ga mutane wanda wani mutum ko gwamnati ta aike shi.
- Yawancin lokaci "wakili" mutum ne da aka bashi iko ya yi wani abu ko ya yi magana a madadin wani mutum da yake wakilta.
- Manzo Bulus ya koyar cewa Kiristoci "jakadu" ne ko kuma "wakilai" tunda shi ke suna wakiltar Kiristi cikin duniyan nan suna kuma koya wa wasu maganarsa.
- Ya danganta kuma ga yadda aka yi amfani da shi a cikin rubutu za a iya fasara shi ya zama "wakilin gwamnati" ko "ɗan aike" ko "zaɓaɓɓen wakili" ko "wakili kirayayyen Allah"
- "Ƙungiyar jakadu" za a iya fassara ta zuwa "wasu manzanni shugabanni." ko " ƙungiyar zaɓaɓɓun wakilai" ko "ƙungiyar mutane 'yan siyasa masu magana domin dukkan mutane."
(Hakanan duba: manzo)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Afisawa 06:20
- Luka 14:31-33
- Luka 19:13-15