1.1 KiB
1.1 KiB
mamaki, al'ajibi, rikicewa
Ma'ana
Dukkan waɗannan kalmomi na fassara ban mamaki ne saboda wani abin da ba a saba gani ba ya faru.
- Waɗansu kalmomin nan fassara ne furcin harshen Girik dake nufin "mamaki ya kama shi" ko "ya tsaya a waje (shi kansa)." Waɗannan furcin sun nuna mafificin mamaki da mutum ya ji. Wasu yare mai yiwuwa suna da tasu irin faɗin idan mamaki ya kama su.
- Yawancin lokaci abin da ya bada mamaki wani abin al'ajibi ne, wani abu da Allah ne kaɗai zai iya yi.
- Wata ma'ana ga kalmomin nan zai iya zama jin ruɗewa domin abin da ya faru ya zo ba zato ba tsammani.
- Wasu hanyoyin fassara waɗannan maganganu sune, "banmamaki" ko "firgicewa ainun."
- Wasu kalmomi kusa a fassararsu sune: "ƙasaitaccen abu mai ɗaukar hankali" ko "ban mamaki" ko "al'ajibi" ko "al'ajibi mai ban mamaki."
- Gabaɗaya dai, duk kalmomin nan suna nuna abu mai kyau ne mutane kuma sun nuna gamsuwa game da abin da ya faru.
(Hakanan duba: al'ajibi, alama)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 08:9-11
- Ayyukan Manzanni 09:20-22
- Galatiyawa 01:06
- Markus 02:10-12
- Matiyu 07:28
- Matiyu 15:29-31
- Matiyu 19:25