721 B
721 B
bagadin turare, turaren bagadi
Ma'ana
Bagadin turare wani sassaƙa ne daga itace wanda firist zai ƙona turare a matsayin baiko ga Allah. Ana kuma kiransa bagadin zinariya.
- Bagadin turare an yi shi ne da katako, samansa da gefunansa an dalaye su da zinariya. Tsawonsa kimamin rabin mita ne, faɗinsa ma rabin mita ne, zurfinsa mita guda ne.
- Da farko an ajiye shi a cikin rumfar sujada. Sa'an nan aka ajiye shi cikin haikali.
- Kowacce safiya da kuma yammaci firist zai ƙona turare akai.
- Za a iya fasara shi haka "bagadi domin ƙona turare" ko, "bagadin zinariya" ko, "wurin ƙona turare" ko, "teburin turare."
(Hakanan duba: turaren ƙonawa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Luka 01:11-13