1.1 KiB
1.1 KiB
faɗakarwa, faɗake-faɗake, faɗake
Ma'ana
Faɗakarwa wani abu ne da yake bada kashedi ga mutane game da wani abin da zai iya cutar su. "A kasance a faɗake" shi ne a zama da damuwa da tsoro game da wani abin dake da hatsari ko neman abkuwa.
- Sarki Yehoshafat ya sami faɗakarwa lokacin da ya ji cewa Mowabawa suna shirin kawo wa masarautar Yahuda hari.
- Yesu ya gaya wa almajiransa kada hankalinsu ya tashi sa'ad da suka ji bala'i na faruwa a ƙarshen kwanaki.
- Wannan furci "sanar da faɗakarwa" ana nufi bada kashedi. A zamanin dã, mutum na iya bada faɗakarwa ta wurin yin ƙãra da wani abu.
Shawarwarin Fassara:
- Idan za a "faɗakar da wani" shi ne "za a sa shi ya damu" ko "a dami wani."
- Zama "a faɗake" za a iya juya shi ya zama "a damu" ko "a tsorata" ko "a damu ainun"
- Furci haka "bada faɗakarwa" za a iya fassara shi ya zama "faɗaka ga jama'a ko "a yi shelar hatsari na zuwa" ko "a busa ƙaho domin a faɗakar cewa hatsari na zuwa."
(Hakanan duba: Yehoshafat, Mowab)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Daniyel 11:44-45
- Irmiya 04:19-20
- Littafin Lissafi 10:9