1.2 KiB
1.2 KiB
tsanantarwa, tsanantawa, tsanani
Ma'ana
Ma'anar "tsanantawa" shi ne a sa wani cikin azaba ko cutarwa. "tsanani" ita ce cuta, ɓacin rai, ko wani bala'i da ya faru domin sa.
- Allah ya tsanantawa mutanensa da cuta ko wasu abubuwa masu wuya saboda su tuba daga zunubansu su juyo gare shi.
- Allah ya sa tsanani ko annobai su abko akan mutanen Masar domin sarkinsu ya ƙi yiwa Allah biyayya.
- "tsanantarwa daga" na nufin shan wuya daga wani abin rashin jin daɗi, kamar ciwo, tsanani, ko ɓacin rai mai sa nishi.
Shawarwarin Fassara:
- Idan ana tsanantawa mutum za a iya cewa "sa mutum ne ya shiga cikin matsaloli" ko "a sa shi ya wahala" ko "a sa wahala ta zo kansa."
- A cikin wasu rubutu "tsanantawa" a iya juyata ta zama da ma'anar "faruwa ga" ko "zuwa ga" ko "kawo wahala"
- Faɗa kamar "tsanantawa wani da kuturta" za a iya juyata ta zama "sa wani ya kamu da ciwon kuturta."
- Bisa ga yadda nassi ya yi amfani da kalman nan "tsanantawa' cikin rubutu za a iya ba ta ma'anar "masifa" ko "ciwo" ko "wahala" ko "babban ƙunci' irin na jiki.
(Hakanan duba: kuturta, annoba, wahala)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 2 Tasalonikawa 01:06
- Amos 05:12
- Kolosiyawa 01:24
- Fitowa 22:22-24
- Farawa 12:17-20
- Farawa 15:12-13
- Farawa 29:32