646 B
646 B
'yantarwa
Ma'ana
Ma'anar "'yantarwa" shi ne furtawa a fili cewa wannan mutum bashi da laifi game da taka shari'a ko halin da bai dace ba wanda ake ƙarar sa akai.
- Ana amfani da kalmar nan a Littafi Mai Tsarki wajen yin magana akan gafarta wa masu zunubi.
- Yawancin lokaci ana magana ne akan rashin gaskiyar 'yantar da mugayen mutane da masu tawaye gãba da Allah.
- A yin fasara za mu iya cewa, "furta rashin aibu" ko "shari'a bata same shi da laifi ba."
(Hakanan duba: gafartawa, laifi, zunubi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Maimaitawar Shari'a 25:1-2
- Fitowa 21:28
- Fitowa 23:07
- Ishaya 05:23
- Ayuba 10:12-14