616 B
616 B
Rami marar matuƙa
Ma'ana
Wannan furci "rami marar matuƙa" babban rami mai zurfi ne ko holoƙon rami da bashi da ƙarshe a zurfi .
- A cikin Littafi Mai Tsarki, "rami marar matuƙa" wurin hukunci ne.
- Misali, idan Yesu ya umarci mugayen ruhohi su fita daga mutum, sukan roƙe shi kada ya aika da su rami marar matuƙa.
- Kalmomin nan "rami marar matuƙa" za a iya juya su zuwa "ramin da babu ƙarshe" ko fili mai zurfi."
- Wannan furci ya sha banban da "wuta," "lahira," ko "jahannama."
(Hakanan duba: Jahannama, lahira, horo)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Luka 08:30-31
- Romawa 10:07