574 B
574 B
Zakiyos
Gaskiya
Zakiyos mai karɓar haraji ne daga Yeriko wanda ya hau bisa itace domin ya ga Yesu wanda taro mai yawa suka kewaye shi.
- Zakiyos ya sami canji na musamman bayan da ya gaskata da Yesu.
- Ya tuba daga zunubinsa na cutar mutane ya kuma yi alƙawarin bãda rabin dukiyarsa ga talakawa.
- Ya kuma yi alƙawarin maido wa mutane har riɓi huɗu kuɗin harajin da ya karɓa daga gare su fiye da kima.
(Hakanan duba: bangaskiya, alƙawari, tuba, zunubi, haraji, mai karɓar haraji)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Luka 19:02
- Luka 19:06