916 B
916 B
Tasalonika, Batasalonike, Tasalonikawa
Gaskiya
A zamanin Sabon Alƙawari, Tasalonika shi ne babban birnin Masidoniya a tsohuwar daular Roma. Mutanen dake zama a wannan birni ake kira "Tasalonikawa."
- Tasalonika birnin ne mai muhimmanci na bakin teku dake kan babbar hanyar da ta haɗe da Roma wajen daular Roma ta gabas.
- Bulus, tare da Silas da Timoti, sun ziyarci Tasalonika a fitar su yawon bishara garo na biyu sakamakon haka kuma, ikilisiya ta kafi a wajen. Daga bisani, Bulus kuma ya ziyarci wannan birni a fitarsa yawon bishara karo na uku.
- Bulus ya rubuta wasiƙu biyu zuwa ga Kiristocin dake Tasalonika. Waɗannan wasiƙu (1 Tasalonikawa da 2 Tasalonikawa) an haɗa dasu cikin Sabon Alƙawari.
(Hakanan duba: Masidoniya, Bulus, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tasalonikawa 01:1
- 2 Tasalonikawa 01:01
- 2 Timoti 04:9-10
- Ayyukan Manzanni 17:01
- Filibiyawa 04:14-17