691 B
691 B
Sukkot
Gaskiya
Sukkot sunan garuruwa biyu ne a Tsohon Alƙawari. Kalmar "sukkot" na nufin "wurin zama."
- Gari na farko ana kiransa Sukkot yana gabas da Kogin Yodan.
- Yakubu ya zauna a Sukkot tare da iyalinsa da garkunansa, ya gina masu wurin zama a nan.
- Bayan shekaru ɗaruruwa, Gidiyon da jama'arsa suka tsaya a Sukkot lokacin da suke yaƙar Midiyanawa, amma mutanen wurin suka ƙi su basu abinci.
- Sukkot na biyun yana arewacin Masar ne kuma a wannan wurin ne Isra'ilawa suka tsaya bayan sun haye Jan Teku lokacin da suke gujewa bauta a Masar.
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sarakuna 07:46
- Fitowa 12:37-40
- Yoshuwa 13:27-28
- Littafin Alƙalai 08: 4-5