707 B
707 B
Simon Zilot
Gaskiya
Simon Zilot na ɗaya daga cikin almajirai goma sha biyu.
- An ambaci Simon sau uku a jeren almajiran Yesu, amma kuma ba ayi cikakken bayani game da shi ba.
- Simon na ɗaya daga cikin sha ɗayan da suka haɗu suka yi addu'a tare a Yerusalem bayan Yesu ya koma sama.
- Kalmar "zilot " na iya zama Simon daga cikin iyalin "Zilotawa", ƙungiyar Yahudawa masu addini da suke da himma riƙe dokar Musa yayin da suke matuƙar tsayayya da gwamnatin Roma.
- Ko, "zilot" na iya zama "himmatattu", ana maganar ƙwazon addinin Simon.
(Hakanan duba: Manzo, almajiri, sha biyun)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 01:12-14
- Luka 06:14-16
- Markus 03: 17-19