680 B
680 B
Silas, Silbanus
Gaskiya
Silas shugaba ne a cikin masu bi na Yerusalem.
- Dattawan ikkilisiya na Yerusalem suka zaɓi Sila da Bulus da Barnaba su kai wasiƙa garin Antiyok.
- Silas daga baya ya tafi tare da Bulus zuwa waɗansu garuruwa don su koyar game da Yesu.
- An sa Bulus da Silas a kurkuku a birnin Filifai. Suka raira yabo ga Allah lokacin da suke a can wurin Allah kuma ya kuɓutar da su daga kurkukun. Yarin ya zama Kirista a ta dalilin shaidarsu.
(Hakanan duba: Antiyok, Barnabas, Yerusalem, Bulus, Filifai, kurkuku, shaida)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Bitrus 05:12
- 1 Tasalonikawa 01:01
- 2 Tasalonikawa 01:01
- Ayyukan Manzanni 15:22