910 B
910 B
Shilo
Gaskiya
Shilo katangar garin Kan'aniyawa ce wadda isra'ilawa suka ci da yaƙi ƙarƙashin shugabancin Yoshuwa.
- Garin Shilo yana yamma da Kogin Yodan da kuma arewa maso gabas da birnin Betel.
- Lokacin da Yoshuwa ke jagorantar Isra'ila, garin shilo ya kasance mahaɗar mutanen Isra'ila.
- Kabilu sha biyu na Isra'ila sukan haɗu a Shilo su saurari Yoshuwa yana faɗa masu rabon kowa daga ƙasar Kan'ana.
- Kafin a gina wani haikali a Yerusalem, a Shilo ne Isra'ilawa kan je su miƙa hadaya ga Allah.
- Lokacin da Sama'ila yake ƙaramin yaro, mahaifiyarsa Hannatu ta ɗaukeshi ta kaishi ya zauna a Shilo don ya horu ta hannun Eli firist ya bautawa Yahweh.
(Hakanan duba: Betel, keɓewa, Hannatu, Yerusalem, Kogin Yodan, firist, hadaya, Sama'ila, haikali)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sarakuna 02: 26-27
- 1 Sama'ila 01:9-10
- Yoshuwa 18: 1-2
- Littafin Alƙalai 18:30-31