590 B
590 B
Shem
Gaskiya
Shem ɗaya daga cikin 'ya'yan Nuhu uku ne, da suka bishi zuwa cikin jirgi lokacin ambaliyar da ta shafe duniya wadda akayi bayaninta a cikin littafin Farawa.
- Shem tsazon Ibrahim ne da zuriyarsa.
- Zuriyar Shem an sansu da "Semiyawa"; suna yin yaren "Semitik" kamar Ibraniyanci da Larabci.
- Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Shem ya rayu kusan shekaru 600.
(Hakanan duba: Ibrahim, Arabiya, Jirgi, ambaliya, Nuhu)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsaki:
- Farawa 05:32
- Farawa 06:10
- Farawa 07:13-14
- Farawa 10:1
- Farawa 10:31
- Farawa 11:10
- Luka 03:36-38