908 B
908 B
Tekun Galili, Tekun Kinneret, Tafkin Genesaret, Tekun Taiberiyas
Gaskiya
"Tekun Galili" tafki ne daga gabas da Isra'ila. A Tsohon Alƙawari ana kiranta da suna "Tekun Kinneret."
- Ruwan wannan tafki na gangarowa zuwa kudu ta cikin Kogin Yodan zuwa Tekun Gishiri.
- Kafarnahum, Betsaida, Genesaret, da kuma Taiberiyas sune garurukan dake daga bakin Tekun Galili a Sabon Alƙawari.
- Yawancin ayyukan da Yesu ya aiwatar a lokacin rayuwarsa sun faru ne kurkusa da Tekun Galili.
- Tekun Galili ana kiransa da suna "Tekun Taiberiyas" da kuma "Tafkin Genesaret."
- Wannan kalma ana fassarata "Tafki a yankin Galili" ko "tafki kusa da Taiberiyas (Genesaret)."
(Hakanan duba: Kafarnihum, Galili, Kogin Yodan, Kogin Gishiri)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Yahaya 06:1-3
- Luka 05:01
- Markus 01:16-18
- Matiyu 04:12-13
- Matiyu 04:18-20
- Matiyu 08:18-20
- Matiyu 13:1-2
- Matiyu 15:29-31