ha_tw/bible/names/samaria.md

1.2 KiB

Samariya, Ba'samariye ko Ba'samariya

Gaskiya

Samariya sunan birni ne da zagayen yankinsa daga arewancin Isra'ila. Yankin na tsakanin kwarin Sharon daga yammansa da kuma Kogin Yodan daga kuma gabas da shi.

  • A Tsohon Alƙawari, Samariya shi ne babban birni na Masarautar Arewancin Isra'ila. Daga baya yankin kewaye da shi aka kira shi da suna Samariya.
  • Sa'ad da Asiriyawa suka mamaye Masarauta ta arewancin Isra'ila, sai suka ƙwace birnin Samariya suka tilasta wa yawancin Isra'ilawa na yankin arewanci su gudu, zuwa wasu birane cikin Asiriya.
  • Asiriyawa suka kawo bãƙi dayawa zuwa cikin yankin Samariya a madadin Isra'ilawa waɗanda aka kora.
  • Wasu daga cikin sauran Isra'ilawa da suka rage a wannan yankin suka auri bãƙin da suka shigo nan, zuriyarsu ana ce da su Samariyawa.
  • Yahudawa suka yi ƙyamar Samariyawa domin su ba cikakkun Yahudawa bane kuma domin kakanninsu sun yi sujada ga kazaman alloli.
  • A zamanin Sabon Alƙawari, yankin Samariya ya yi iyaka da yankin Galili daga arewacinsa da kuma yanki na Yahudiya daga gabas.

(Hakanan duba: Asiriya, Galili, Yahudiya, masarautar Isra'ila)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 08:1-3
  • Ayyukan Manzanni 08:05
  • Yahaya 04:4-5
  • Luka 09:51-53
  • Luka 10:33