725 B
725 B
Ramot
Gaskiya
Ramot birni ne mai muhimmanci a cikin tsaunukan Giliyad kusa da Kogin Yodan. Ana kuma kiran sa da suna Ramot Giliyad.
- Ramot gãdo ne na Isra'ilawa kabilar Gad an kuma keɓe shi birnin mafaka.
- Sarki Ahab na Isra'ila da Sarki Yehoshafat na Yahuda sun yi yaƙi gãba da sarkin Aram a Ramot. An kashe Ahab a wannan yaƙi.
- Akwai wani lokacin da, Sarki Ahaziya da Sarki Yoram suka yi yunƙurin su mallaki birnin Ramot daga sarkin Aram.
- A Ramot Giliyad aka shafe Yehu sarki bisa Isra'ila.
(Hakanan duba: Ahab, Ahaziya, Gad, Yehoshafat, Yehu, Yoram, Kogin Yodan, Yahuda, mafaka)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Tarihi 06:73
- 1 Sarakuna 22:03
- 2 Tarihi 18:03
- 2 Sarakuna 08:28-29