711 B
711 B
Fontus
Gaskiya
Fontus wani lardin Roma ne a lokacin mulkin Roma da Ikilisiya ta farko. An kafa ta ne a kudancin gaɓar Baƙin Teku, a arewacin yankin da yanzu ita ce ƙasar Turkaniya ko Toki.
- Kamar yadda yake a rubuce a littafin Ayyukan Manzanni, mutane da suke daga lardin Fontus suna Yerusalem sa'ad da Ruhu Mai Tsarki ya fara zuwa ga manzanni a Ranar Fentikos.
- Wani mai bada gaskiya mai suna Akila ya zo ne daga Fontus.
- Lokacin da Bitrus yake rubuta wa Kiristoci dake warwatse cikin wurare daban-daban na yankin nan, Fontus na ɗaya daga cikin yankunan daya ambata.
(Hakanan duba: Akila, Fentikos)
Wuraren da za ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Bitrus 01:1-2
- Ayyukan Manzanni 02:09