885 B
885 B
Fenihas
Gaskiya
Fenihas sunan mutum biyu ne a cikin Tsohon Alƙawari.
- Wani firist mai suna Fenihas yana ɗaya daga cikin jikokin Haruna maza. Yayi gãba sosai da bautar gumaku a Isra'ila.
- Fenihas ya ceci Isra'ilawa daga annobar da Yahweh ya aika domin ya hukunta su domin sun auri matan Midiyawa suka yi wa allolinsu sujada.
- Fenihas ya tafi tare da sojojin Isra'ilawa sau da yawa domin su hallaka Midiyawa.
- Wani Fenihas da aka ambata a Tsohon Alƙawari ɗaya ne daga cikin mugayen 'ya'yan Eli firist a zamanin annabi Sama'ila.
- Fenihas da ɗan'uwansa Hofni an kashe dukkan su biyun sa'ad da Filistiyawa suka kai wa Isra'ila hari suka sace Akwatin Alƙawari.
(Hakanan duba: akwatin alƙawari, Kogin Yodan, Midiyawa, Filistiyawa, Sama'ila)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sama'ila 04:04
- Ezra 08:02
- Yoshuwa 22:13-14
- Littafin Lissafi 25:6-7