783 B
783 B
Filistiyawa
Gaskiya
Filistiyawa wasu ƙungiyar mutane ne da suka zauna a yankin Filistiya a gaɓar Tekun Baharmaliya. Ma'anar sunansu "mutanen teku."
- Akwai manyan biranen Filistiya guda biyar: Ashdod, Ashkelon, Ekron, Gat, da Gaza.
- Birnin Ashdod yana arewacin sashen Filistiya, birnin Gaza kuma yana kudunta.
- Alƙali Samson shahararren mayaƙi ne gãba da Filistiyawa, ya yi amfani da mafificin ƙarfi daga Allah.
- Sarki Dauda yawancin lokaci yakan kai yaƙi ga Filistiyawa, har da lokacin da yake saurayi ya buge mayaƙin Filistiya, Goliyat.
(Hakanan duba: Ashdod, Ashkelon, Dauda, Ekron, Gat, Gaza, Goliyat, Tekun Gishiri)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1Tarihi 18:9-11
- 1 Sama'ila 13: 04
- 2 Tarihi 09:25-26
- Farawa 10:11-14
- Zabura 056:1-2