680 B
680 B
Fir'auna, sarkin Masar
Gaskiya
A zamanin dã, sarakunan da suka yi mulki a Masar ana ce da su Fir'aunnoni.
- Gaba ɗaya duka, fir'aunoni sama da 300 suka yi sarautar Masar fiye da shekaru 2,000.
- Waɗannan sarakunan Masar masu iko ne da wadata.
- Da yawa cikin waɗannan fir'aunonin an faɗe su a cikin Littafi Mai Tsarki.
- Yawancin lokaci wannan muƙamin ana amfani da shi a maimakon suna. Idan haka ya faru akan fara rubutawa da babban harufa kamar haka, "Fir'auna."
(Hakanan duba: Masar, sarki)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ayyukan Manzanni 07:9-10
- Ayyukan Manzanni 07:13
- Ayyukan Manzanni 07:21
- Farawa 12:15
- Farawa 40:07
- Farawa 41:25