897 B
897 B
Fasiya, Fasiyawa
Gaskiya
Fasiya ƙasa ce wadda ita ma ta zama babbar mulki mai iko wadda Sairus Mai Girma ya kafa a shekara ta 550 BC. Ƙasar Fasiya tana kudu maso gabas da Babiloniya da kuma Asiriya a yankin da yau ake ce da shi Iran.
- Mutanen Fasiya ana ce da su "Fasiyawa."
- A ƙarƙashin dokar Sarki Sairus, aka 'yantar da Yahudawa daga bautar talala a Babila aka yardar masu su tafi gida, kuma aka sake gina haikali a Yerusalem, da kuɗin da mulkin Fasiya ya tanada.
- Sarki Atazazas shi ne mai mulkin sarautar Fasiya lokacin da Ezra da Nehemiya suka koma Yerusalem domin su sake gina ganuwoyin Yerusalem.
- Esta ta zama sarauniyar mulkin Fasiya lokacin data auri Sarki Ahasurus.
(Hakanan duba: Ahasurus, Atazazas, Asiriya, Babila, Sairus, Esta, Ezra, Nehemiya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 2 Tarihi 36:20
- Daniyel 10:13
- Esta 01:3-4
- Ezekiyel 27:10