685 B
685 B
Feyo, Tsaunin Feyo, Ba'al Feyo
Gaskiya
Wannan magana "Feyo" da "Tsaunin Feyo" ana ambaton wani tsauni ne dake arewa maso gabas da Tekun Gishiri, a yankin Mowab.
- Wannan suna "Bet Feyo" sunan wani birni ne, da aka kafa watakila akan tsaunin ko kusa da shi. A nan ne Musa ya rasu bayan da Allah ya nunan masa Ƙasar Alƙawari.
- "Ba'al Feyo" gunkin Mowabawa ne da suke yi masa sujada akan Tsaunin Feyo. Isra'ilawa suma sun fara yiwa wannan gunki sujada Allah kuma ya hukunta su akai.
(Hakanan duba: Ba'al, gunki, Mowab, Tekun Gishiri, sujada)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Littafin Lissafi 23:28-30
- Littafin Lissafi 31:16-17
- Zabura 106:28 -29