1.3 KiB
1.3 KiB
Bulus, Saul
Gaskiya
Bulus shugaba ne na ikilisiya ta farko wanda Yesu ya aike shi ya kai wannan labari mai daɗi zuwa ga wasu ƙungiyoyin mutane da yawa.
- Bulus Bayahude ne wanda an haife shi cikin birnin Tarsus ta Roma, ya kuma zauna a can domin ɗan ƙasar Roma ne.
- Tun farko ana kiran Bulus da sunansa na Yahudanci, Saul.
- Saul ya zama shugaban addinin Yahudawa ya danƙe Yahudawa da suka zama Kirista domin yana tsammani suna nuna rashin bangirma ga Allah ta wurin gaskantawa da Yesu.
- Yesu ya bayyana kansa ga Saul a wani haske mai makantarwa ya gaya masa ya dena cutar da Kiristoci.
- Saul ya bada gaskiya ga Yesu sai ya fara koyar da 'yan'uwansa Yahudawa akan Yesu.
- Daga baya, Allah ya aiki Saul ya koyar da mutanen daba Yahudawa bane akan Yesu, ya kuma fara kafa ikilisiyoyi a birane daban-daban a lardunan mulkin Roma. A wannan lokaci ne aka fara kiransa da sunansa na Romanci "Bulus."
- Bulus kuma ya rubuta wasiƙu domin ya ƙarfafa ya kuma koyar da Kiristocin dake cikin ikkilisiyoyi a biranen nan. Yawancin wasiƙun nan suna cikin Sabon Alƙawari.
(Hakanan duba: Kirista, shugabannin yahudawa, Roma)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Korantiyawa 01:03
- Ayyukan Manzanni 08:03
- Ayyukan Manzanni 09:26
- Ayyukan Manzanni 13:10
- Galatiyawa 01:01
- Filimon 01:08