883 B
883 B
Nuhu
Gaskiya
Nuhu mutum ne da ya yi rayuwa wajen sama da shekaru 4,000 da suka wuce, a lokacin da Allah ya aiko da ambaliyar ruwa da ya game duniya dukka ya hallaka dukkan mugayen mutane dake a duniya. Allah ya ce wa Nuhu ya gina wani makeken jirgi wanda shi da iyalinsa zasu zauna a ciki sa'ad da ruwa ya rufe fuskar duniya.
- Nuhu adilin mutum ne wanda ya yi biyayya da Allah cikin dukkan abu.
- Da Allah ya ce Nuhu ya gina makeken jirgi, Nuhu ya gina shi dai-dai yadda Allah ya gaya masa ya yi.
- A cikin jirgin ne , aka kiyaye Nuhu da iyalinsa lafiya, daga baya 'ya'yansu da jikokinsu suka sake cika duniya da mutane.
- Kowanne mutum da aka haifa tun daga lokacin ruwan tsufana zuriyar Nuhu ne.
(Hakanan duba: zuriya, jirgi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Farawa 05:30-31
- Farawa 05:32
- Farawa 06:08
- Farawa 08:01
- Ibraniyawa 11:7
- Matiyu 24:37