904 B
904 B
Nehemiya
Gaskiya
Nehemiya Ba'isra'ile ne da dole ya tafi ƙasar Babiloniya sa'ad da Babiloniyawa suka kwashe mutanen Isra'ila da Yahuda zuwa bautar talala.
- Lokacin da yake Mai shayarwa ga Sarkin Fasiya, Atazazas, Nehemiya ya roƙi sarki iznin ya koma Yerusalem.
- Nehemiya ya bida Isra'ilawa a gina ganuwar Yerushalem wanda Babiloniyawa suka rushe.
- Nehemiya yayi shekara goma sha biyu yana shugabanci a Yerusalem kafin ya koma fadar sarki.
- Littafin Nehemiya a Tsohon Alƙawari ya bada labarin ayyukan Nehemiya na sake gina ganuwa da shugabantar da mutanen Yerusalem.
- Akwai kuma wasu mutane masu sunan Nehemiya a Tsohon Alƙawari. Yawancin lokaci akan ƙara da sunan mahaifi domin a banbanta wane Nehemiyan ake magana a kai.
(Hakanan duba: Atazazas, Babila, Yerusalem, ɗa)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Ezra 02:1-2
- Nehemiya 01:02
- Nehemiya 10:03
- Nehemiya 12:46