721 B
721 B
Na'aman
Gaskiya
A cikin Tsohon Alƙawari, Na'aman shi ne shugaban rundunar mayaƙan sarkin Aram.
- Na'aman yana da mummunan ciwon fatar jiki da ake kira kuturta da ba a iya warkarwa.
- Wata baiwa Ba'yahudiya a cikin gidan Na'aman ta gaya masa, ya je ya roƙi annabi Elisha ya warkar da shi.
- Elisha ya ce wa Na'aman ya yi wanka sau bakwai a Kogin Yodan. Da Na'aman ya yi biyayya, Allah ya warkar da shi daga cutar.
- Sakamakon haka, Na'aman ya gaskanta da Allah kaɗai na gaskiya Yahweh.
- Wasu mazaje biyu da ake kiransu Na'aman zuriyar ɗan Yakubu ne Benyamin.
(Hakanan duba: Aram, Kogin Yodan, kuturta, annabi)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Tarihi 08:6-7
- 2 Sarakuna 05:01
- Luka 04:27