633 B
633 B
Modakai
Gaskiya
Modakai Bayahuden mutum ne da ya zauna a ƙasar Fasiya. Shi ne mai lura da ɗiyar ɗan'uwansa Esta, wadda daga bisani ta zama matar sarkin Fasiya, Ahasurus.
- Sa'ad da yake aiki a fadar masarauta, Modakai ya ji mutane na shirin su kashe sarki Ahasurus. Ya je ya fallasa wannan al'amari ran sarki ya tsira.
- Bayan wannan, Modakai kuma ya gano shirin da ake yi domin a kashe dukkan Yahudawa a mulkin Fasiya. Ya ba Esta shawara ta roƙi sarki ya ceci mutanenta.
(Hakanan duba: Ahasurus, Babila, Esta, Fasiya)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- Esta 02:06
- Esta 03:06
- Esta 08:02
- Esta 10:02