622 B
622 B
Molek, Molok
Gaskiya
Molek sunan ɗaya daga cikin gumakun da Kan'aniyawa suke yiwa sujada. Wasu sukan rubuta shi haka "Molok" da "Molek."
- Mutanen dake yiwa Molek sujada suna miƙa masa 'ya'yansu hadaya ta wurin wuta.
- Wasu Isra'ilawa kuma sun yi wa Molek sujada maimakon Allah na gaskiya, Yahweh. Suka bi ayyukan mugunta na masu yiwa Molek sujada. har ma da miƙa 'ya'yansu hadaya.
(Hakanan duba: Kan'ana, mugunta, gunki, Allah, hadaya, gaskiya, sujada, Yahweh)
Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
- 1 Sarakuna 11:07
- 2 Sarakuna 23:10
- Ayyukan Manzanni 07:10
- Irmiya 32:33-35
- Lebitikus 18:21